Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-06 17:15:41    
Kasar Sin ta tamaka sauran kasashe masu tasowa ba tare da sharadin siyasa ba

cri

Ran 6 ga wata, Mr. Li Zhaoxing, ministan harkokin waje na kasar Sin ya nuna cewa, yayin da kasar Sin tana neman bunkasuwarta, tana ba da taimakawa a zihiri ga sauran kasashe masu tasowa ba tare da sharadin siyasa ba.

A gun taron manema labaru na taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'a, Mr. Li Zhaoxiang ya ce, kasar Sin tana bunkasawa ta hanyar zaman lafiya, kuma tana taka muhimmiyar rawa kan harkokin duniya. Kasar Sin tana son ta yi shawarwarin abokantaka mai daidaiwuwa tare da kasashen Afirka da sauran kasashen duniya.

Game da batun Darfur na kasar Sudan, Mr. Li Zhaoxing ya ce, yayin da shugaba Hu Jintao ke yin ziyara a kasar Sudan, ya bayyana matsayin gwamnatin kasar Sin. Kuma gwamnatin kasar Sin tana goyon bayan ra'ayin iri daya da MDD, da kungiyar AU, da gwamnatin Sudan suka samu. kuma sau da dama gwamnatin kasar Sin ta taba ba da taimakon tausayin 'dan Adam ga jama'an yankin Darfur. Kasar Sin tana fatan kasashen duniya su yi kokari don ba da taimakawa a zahiri ga yankin Darfur.