Shirin rahoton kasafin kudi da ma'aikatar kudi ta kasar Sin ta mika ga wakilan jama'ar kasar Sin don yin bincike a ran 5 ga wata ya nuna cewa, a shekarar nan da muke ciki, kasar Sin ta ware kudin Sin yuan biliyan 23 a fannin harkokin waje don kara yin mu'amala da hadin gwiwa a tsakaninta da kasashen waje, wanda ya karu da fiye da kashi 37 cikin kashi dari bisa na makamancin lokaci na bara.
Dalilan da suka sa kasar Sin ta kara kashe kudi kan harkokin waje a bana su ne domin za ta kara bai wa kasashen Afirka kudin taimako, bisa tunanin taron dandalin hadin gwiwa a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, sa'an nan kuma, za ta kara bai wa kungiyoyin kasa da kasa kudin karo-karo don zama mamba na kungiyoyi da hukumomi da kudade domin ayyukan kiyaye zaman lafiya, haka kuma, za ta yi gyare-gyare kan albashin ma'aikatan ofisoshin jakadanci nata a kasashen waje.
A ran 5 ga wata, a nan Beijing, a lokacin da yake zantawa da manema labaru, ma'aikacin jakadanci na kasar Guinea a nan Beijing Senkoun Sylla a kasar Sin ya yi bayani kan kara bai wa Afirka taimako da kasar Sin za ta yi, ya ce, kasashen Sin da Afirka suna kara hada kansu, kara bai wa kasashen Afirka taimako da kuma daukaka ci gaban muhimman ayyuka a Afirka suna amfana wajen bunkasuwar dukan bangarorin Sin da Afirka.(Tasallah)
|