Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-05 21:30:39    
Shugabannin Sin sun sa ran gaggauta bunkasuwar tattalin arzikin wurare daban daban na kasar

cri
A yau Litinin, ranar 5 ga wata, Hu Jintao da Wu Bangguo da Jia Qinglin da Zeng Qinghong, da dai sauran shugabannin jam'iyyar kwaminis ta Sin kuma shugabannin kasar, sun duba rahoton ayyukan gwamnati tare da sauran 'yan tawagogin wakilan wurare daban daban da suke ciki, kuma sun nemi wadannan larduna da shiyyoyi da su yi amfani da damar da ke gabansu, su gaggauta bunkasuwar tattalin arziki, kuma su kara mai da hankulansu kan daidaita batutuwan da ke shafar zaman rayuwar jama'a.

A yanzu haka dai ana yin taron shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a nan birnin Beijing, wato hukumar koli ta kasar. A ran nan da yamma, a yayin da shugaban kasar Sin, Hu Jintao ke duba rahoton ayyukan gwamnatin tare da 'yan tawagar wakilan jihar Tibet, ya yi fatan shugabanni da talakawa 'yan kabilu daban daban na Tibet za su yi amfani da damar da ke gabansu na aiwatar da manufar bunkasa yankunan yammacin kasar Sin da kara karfin ba da taimako ga Tibet da gwamnatin kasar ke yi, su yi amfani da taimakon da aka ba su yadda ya kamata, don kara bunkasa karfin kansu. Mr.Hu Jintao ya kuma jaddada cewa, ya kamata a dora muhimmanci sosai a kan daidaita batutuwan da ke shafar zaman rayuwar jama'a, a gudanar da ayyukan da ke shafar kabilu da addinai yadda ya kamata, a yi kokari ba tare da kasala ba don tabbatar da kwanciyar hankali mai dorewa da zaman alheri a Tibet.(Lubabatu)