Yau a nan birnin Beijing, shugaban babban bankin kasar Sin, Mr.Zhou Xiaochuan ya bayyana cewa, matsayin kudin ruwa da Sin ke aiwatarwa ya dace.
A yayin da yake halartar taron shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, Mr.Zhou Xiaochuan ya ce, a shekara ta 2006, don neman dacewa da manufar kasa ta daidaita tattalin arziki daga manyan fannoni, babban bankin kasar Sin ya taba daga matsayin kudin ruwa na kudin Sin har sau biyu, kuma matsayin kudin ruwa da ake aiwatarwa a halin yanzu yana dacewa da bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin. Ya ce, bisa bukatun bunkasuwa, Sin za ta gyara tattalin arzikinta ne ta hanyar daidaita kudin ruwanta da darajar kudinta.(Lubabatu)
|