|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2007-03-05 18:24:39
|
 |
Gwamnatin kasar Sin za ta ci gaba da sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar da ke tsakanin bangarori 2 na mashigar teku na Taiwan bisa manufar Sin daya tak
cri
A gun taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar duk kasar Sin da aka bude a ran 5 ga wata, a lokacin da ya ke gabatar da rahoton ayyukan gwamnatin, Mr. Wen Jiabao, firayin ministan kasar ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin za ta ci gaba da karfafa yin tattaunawa da cudanya tare da jam'iyyu daban daban na Taiwan, wadanda ke tsayawa kan bunkasa dangantakar da ke tsakanin bangarori 2 na mashigar teku na Taiwan, bisa manufar Sin daya tak, domin neman sake maido da tattaunawa da shawarwari a tsakanin bangarorin biyu tun da wuri, da sa himma domin ganin bunkasa dangantakar da ke tsakanin bangarorin biyu kamar yadda ya kamata.
Mr. Wen Jiabao ya ce, babban yankin kasar Sin zai hada kai tare da dimbin 'yan uwanmu na Taiwan, domin tsayawa kan matsayin adawa da duk wani yunkuri na neman "yancin kan Taiwan bisa doka", da kuma sauran ayyukan kawo baraka, bisa batun bunkasuwar dangantakar da ke tsakanin bangarori 2 na mashigar teku na Taiwan cikin lumana, da sa kaimi ga ayyukan yin cudanya da hadin kai a tsakanin bangarorin biyu, da kuma sa himma domin ganin cinikayya, da aikawa da wasiku, da kuma sufurin jiragen sama a tsakanin bangarorin biyu kai tsaye, za su yi iyakacin kokari don neman zaman lafiya, da bukasuwa, da kuma jin dadi ga 'yan uwa na bangarorin biyu.
Bayan haka kuma, Mr. Wen Jiabao ya sake nanata muhimmiyar manufar "sake hadewa cikin lumana, da kasa daya mai tsarin mulki biyu" da gwamnatin Sin take tsayawa, wajen warware matsalar Taiwan. (Bilkisu)
|
|
|