Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-05 18:22:32    
Kasar Sin za ta yi kokari kan sassauta matsalar da rarar ciniki ke kawowa

cri
A gun taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar duk kasar Sin da aka bude a ran 5 ga wata, a lokacin da ya ke gabatar da rahoton ayyukan gwamnatin, Mr. Wen Jiabao, firayin ministan kasar ya bayyana cewa, kasar Sin za ta kyautatta tsarin shigi da fici, da juya hanyar bunkasuwar cinikin waje, domin sassauta matsalar da rarar cinikin waje ke kawowa.

Mr. Wen Jiabao ya ce, kasar Sin tana goyon bayan fitar da kayyayaki masu alamu na kansu, da kuma ke da inganci.
Yawan rarar cinikin waje ta kasar Sin ya wuce dollar Amurka biliyan 170.

Bayan haka kuma, Mr. Wen Jiabao ya bayyana cewa, kasar Sin za ta jagoranci daidaita masana'antun kasar wajen hadin kan zuba jari a waje, da kafa yankunan hadin kai na tattalin arziki da ciniki a kasashen waje masu kyau, da sa kaimi ga kafuwar yankunan cinikayya maras shinge a tsakanin bangarori biyu da shiyya-shiyya. Bayan haka kuma, kasar Sin za ta kara matsayin bude kofa ga kasashen waje a fannin sha'anin kudi, da kuma kara sanya ido, domin kaucewa hadarin harkokin kudi.

Bayan haka kuma, ya jaddada cewa, kasar Sin za ta dauki matakai a fannoni daban daban, domin sassauta halin rashin daidaituwar kudaden musaya da take samu sannu a hankali. (Bilkisu)