
Ran 5 ga wata, A ran 5 ga wata da safe, an soma taron shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar duk kasar Sin, wato hukumar koli ta dokokin kasar Sin, a nan birnin Beijing. Mr. Wen Jiabao, firayin ministan kasar Sin ya gabatar da wani rahoto kan aikin gwamnati inda ya nuna cewa, ya kamata a bunkasa sha'anin gina gidajen kwana ga kowa, kuma ya kamata gwamnatin kasar Sin ta warware matsalar gidajen kwana ga jama'a masu talauci.

Mr. Wen Jiabao ya kara cewa, gwamnatin kasar Sin za ta kara yi kokari don kafa wani tsarin gidajen haya masu arahusa, kuma kyautata tsarin gidajen kwana masu arahusa.
Game da batun "farashin gidajen kwana ya yi ta karuwa da sauri", Mr. Wen ya ce, gwamnatin kasar Sin za ta kara dauki matakai don hana saurin karuwar farashin farashin gidajen kwana, kuma mai da farashin a matsayin yadda ya kamata, kuma za ta kara zurfafa kuma daidaita tsarin kasuwar gidajen kwana.
|