Firayin ministan kasar Sin Wen Jiabao ya bayyana cewa, lokacin da ake kyautata tsarin masana'antu da kara neman riba da rage makamashin da ake amfani da shi tare da kuma kiyaye yanayin daukar sauti, ana fatan kimanin karuwar kudaden da aka samu daga aikin kawo albarkar cikin gida, wato GDP zai kai kashi 8 cikin kashi dari a shekarar da muke ciki. Wannan ne karo na farko da kasar Sin ta tabbatar da sharuda wajen neman cigaban tattalin arzikinta.
Wen Jiabao ya fadi haka ne a cikin rahoto kan aikin gwamnati da ya bayar a gun bikin kaddamar da taron shekara-shekara na majalisar dokokin kasar Sin da aka fara yi yau, ran 5 ga wata.
Wen Jiabao ya kuma ce, abin da ya fi muhimmanci shi ne za a mayar da tunanin jama'a da su nemi cigaban tattalin arziki bisa ilmin kimiyya, da kuma su sanya aikin kyautata tsarin masana'antu da kara neman riba da yin tsimin makamashi da rage fitar da abubuwan da ke gurbata muhalli a kan muhimman ayyukan da za su yi. Mr. Wen yana fatan kada a nemi saurin karuwar tattalin arziki ba bisa ilmin kimiyya ba. Sabo da haka. Yana fatan za a iya samun cigaban tattalin arziki mai kyau kuma cikin sauri. (Sanusi Chen)
|