A ran 5 ga wata da safe, an soma taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'r duk kasar Sin, wato hukumar koli ta dokokin kasar Sin, a nan birnin Beijing. Shugabannin kasar Sin ciki har da shugaban kasa Hu Jintao da shugaban majalisar dokoki Wu Bangguo da firayin minista Wen Jiabao da wakilan jama'a kusan dubu 3 sun halarci bikin kaddamar da taron. A gun taron, za a dudduba tare da kuma yanke shawara kan shirin "Dokar Ikon Mallakar Dukiyoyi" da "Dokar Buga haraji kan masana'antu".
Mr. Wu Bangguo, shugaban zaunannen kwamitin majalisar dokokin kasar Sin ne ya shugabanci bikin kaddamar da taron. Mr. Wen Jiabao, firayin ministan kasar Sin ya gabatar da wani rahoto kan aikin gwamnati ga wakilan jama'a kusan dubu 3 a madadin gwamnatin tsakiya. A cikin rahatonsa, da farko dai, Mr. Wen ya waiwayi ayyukan da gwamnatin ta yi a cikin shekarar da ta gabata da ayyukan da za ta yi a shekarar da muke ciki. Sannan kuma, abubuwan da wannan rahoto ke kunshe da su suna shafar ayyukan tsaron kasa da raya rundunar soja da batutuwan Hong Kong da Macao da Taiwan tare da kuma manufofin diplomasiyya da kasar Sin ke aiwatarwa.
Bisa ajandar da aka tsara, a gun taron da za a yi kwanaki 11 ana yinsa, wakilan jama'a za su dudduba tare da kuma jefa kuri'a kan shirye-shirye 2 na "Dokar Ikon Mallakar Dukiyoyi" da "Dokar Buga Haraji kan Masana'antu". Bugu da kari kuma, za su dudduba da jefa kuri'a kan rahoton aiki na shekara-shekara na gwamnati da na zaunannen kwamitin majalisar dokokin kasar da na kotun koli ta jama'a da hukumar koli ta bincike ta jama'a da rahoton kasafin kudi na kasar. (Sanusi Chen)
|