
Da karfe 9 na ran 5 ga watan Maris da safe, an soma cikakken zama na 5 , wato taron shekara-shekara na majalisar dokokin kasar Sin ta 10 a babban dakin taruwar jama'a na Beijing, inda firayin ministan kasar Sin Wen Jiabao ya bayar da rahoton aikin gwamnatin.

Bisa ajandar da aka tsara, za a rarraba wa wakilan majalisar rahotanni yadda majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta aiwatar da shirin raya tattalin arziki da zaman al'umma na shekarar 2006 da yadda za ta aiwatar da shirin raya tattalin arziki da zaman al'umma na shekarar 2007, tare da kuma rahoton yadda majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta yi amfani da kasafin kudi na gwamnatin tsakiya da na wurare daban-daban a shekarar 2006 da yadda za ta yi amfani da kasafin kudi a shekarar 2007.
Gidan rediyon kasar Sin, wato CRI da gidan rediyon jama'ar kasar Sin da gidan talabijin na kasar Sin za su yada labaru game da wannan bikin kaddamar da taron shekara-shekara kai tsaye. Shafuffukan internet na gwamnatin kasar Sin da Xinhua da People's Daily da na China za su kuma yada labari cikin lokaci. (Sanusi Chen)
|