Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-04 21:08:01    
Shugabannin Sin sun kai ziyara ga wakilai mahalartan taron majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar

cri
Ran 4 ga wata, Hu Jintao da Wu Bangguo da Wen Jiabao da Jia Qinglin da sauran shugabannin Jan'iyyar Kwaminis ta Sin da na gwamnatin kasar sun kai ziyara ga wakilai mahlartarn taro na biyar na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin ta goma bi da bi, kuma sun shiga shawarari da taron ya yi cikin kungiya-kungiyar, a tsanake suka saurari ra'ayoyi da shawarari da wakilan suka gabatar a kan manyan harkokin siyasa da manufofi na kasar da batutuwa da suka fi jawo hankulan jama'a.

A gun taron da jam'iyyar manoma da ma'aikata ta kasar Sin da jam'iyyar Jiu San suka shirya cikin hadin guiwarsu, Hu Jintao, shugaban kasar Sin ya yi jawabi musamman a kan gaggauta bunkasa harkokin kiwon lafiya. Ya jaddada cewa, ya kamata, a yi kokari wajen cim ma manufar ba da magani ga duk jama'ar kasar baki daya, a yi daga matsayin kiwon lafiyar jama'a.

A gun wani taro dabam da bangarorin tattalin arziki da na aikin noma suka shirya, firayim minista Wen Jiabao ya bayyana cewa, ya kamata, ma'aikatan gwamnati wadanda suka halarci taron majalisar wakilan jama'ar kasa da na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar su saurari ra'ayoyi da shawarwari da aka gabatar a kan fannoni daban daban, su kuma bayyana ayyukan gwamnati bisa halin da ake ciki, su yi kokari wajen yin bincike kan shirin batutuwa da shawarwari da wakilan suka gabatar a kan ayyukan gwamnati, don kyautata ayyukan gwamnatin. (Halilu)