Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-04 20:28:18    
A galibi dai kasafin kudi da kasar Sin ta yi a fannin tsaron kasa a bana ya yi daidai da na shekarun baya

cri
Ran 4 ga wata, a nan Beijing, kakakin taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Mr. Jiang Enzhu ya bayyana cewa, a shekarar bana, kasafin kudi a fannin tsaron kai a shekara ta 2007 da majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta gabatar da shi ga taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin don yin bincike da amincewa ya kai misalin kudin Sin yuan biliyan 350.9, wanda ya kai kashi 7.5 cikin kashi dari bisa jimlar kasafin kudi da gwamnatin Sin ke kashewa a bana, a galibi dai wannan adadi ya yi daidai da na shekarun baya da suka wuce.

Mr. Jiang ya jaddada cewa, ko kudaden da kasar Sin take amfani da su a fannin tsaron kanta, ko kuma yawan kashi da kudaden suka dauka bisa jimlar kudaden shiga da kasar Sin ta samu, da jimlar kudi da Sin take samu daga aikin kawo albarka, dukansu sun yi kadan. Ya kuma nanata cewa, kasar Sin na tsayawa tsayin daka kan bin hanyar samun bunkasuwa cikin lumana, tana nacewa ga aiwatar da manufofin tsaron kasa bisa ka'idar tsaron kanta. (Tasallah)