|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2007-03-04 16:25:22
|
Gobe, za a bude taron shekarar nan na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin
cri
Ran 5 ga wata, za a bude taron shekarar nan na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a nan birnin Beijing. Yanzu, yawan 'yan majalisar wadanda suka riga suka zo nan birnin Beijing ya kai 2,943. A gun taron nan na kwanaki 11 da rabi, 'yan majalisar za su yi bincike a kan shirin dokoki biyu wato doka kan ikon mallakar dukiyoyi da doka kan harji da ake bugawa a kan kudin shiga da masana'antu ke samu.
Ban da wadannan dokoki biyu, taron zai yi bincike a kan rahoto da za a gabatar dangane da halin kudi na gwamnatin kasar, da saurari rahoto kan ayyukan gwamnati da rahotanni kan ayyukan shekara na babban kotun jama'ar kasar da babbar hukumar gabatar da kara ta jama'ar kasar da zaunannen kwamitin majalisar, kuma taron zai yi bincike a kan rahotonnin da jefa kuri'u a kai. (Halilu)
|
|
|