Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-19 17:10:30    
Kasar Sin tana ba da jagoranci ga fararren hula wajen yin haihuwa bisa tsarin ta bin manufofin ba da gatanci

cri

Kasar Sin wata kasa ce da yawan mutanenta ya kai biliyan 1.3. Bayan shekaru 70 na karnin da ya gabata, kasar Sin ta fara aiwatar da manufar haihuwa bisa tsari domin rage karuwar yawan mutane cikin sauri. Domin aiwatar da manufar yadda ya kamata da kuma kula da zaman rayuwar fararren hula, a 'yan shekarun nan da suka gabata, kasar Sin ta yi gwajin wata sabuwar manufar haihuwa bisa tsari a kauyukan kasar Sin, wato na bayar da kyautar kudi a matsayin yabo ga mutanen da ke bin manufar haihuwa bisa tsari, ta yadda za ta iya ba da jagoranci ga fararren hula wajen haihuwa bisa tsari bisa son rai. Haka kuma an samu sakamako mai kyau bayan da aka aiwatar da manufar. To, a cikin shirinmu na yau, za mu yi muku bayani kan batun.

Luo Cui'an 'yar shekaru 69 da haihuwa wata tsohuwa ce a jihar Yunnan da ke kudu maso yammacin kasar Sin. Tana da diya guda daya. Yanzu ban da alawas da aka ba ta don ritaya, Madam Luo tana iya kara samun yuan 700 a ko wace shekara. Ta gaya wa wakilinmu cewa,

"bayan da aka aiwatar da irin wannan kyakkyawar manufa, a cikin shekaru biyu da suka gabata, ina samun yuan 700 a ko wace shekara. Sabo da haka na yi farin ciki sosai."


1 2 3