Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-10 16:09:57    
Hu Jintao ya fara yin ziyarar aiki a kasar Seychelles

cri

Shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya isa birnin Victoria, babban birnin kasar Seyshelles, don fara yin ziyarar aiki a kasar, bisa gayyatar da takwaransa na kasa Mr. James Alix Michel ya yi masa. Wannan shi ne karo na farko da shugaban kasar Sin ya kai ziyara a Seyshelles.

A filin jirgin sama, shugaba Michel ya shirya gagarumin bikin maraba da zuwan shugaba Hu Jintao. A lokacin da ya yi jawabi a rubuce a filin jirgin sama, shugaba Hu ya ce, tun bayan da kasashen Sin da Seyshelles suka kulla huldar diplomasiya na shekaru 30, sun nuna girmama ga juna, kuma sun zaman daidai wa daida, sun yi ta kara samun ci gaba wajen hakikanin hadin kai a tsakaninsu a fannoni daban daban, sun kiyaye shawarwari da daidaituwa a cikin harkokin kasashen duniya. Ya bayyana imani cewa, ko shakka babu, ziyarar nan za ta karfafa zumunci a tsakanin kasashen Sin da Seyshelles, da habaka kyakkyawan hadin kai a tsakanin bangarorin biyu, da kuma sa kaimi ga bunkasuwar kasashen biyu tare.

Kasar Seyshelles ita ce ta karshe a cikin jeren kasash 8 na Afrika da shugaba Hu yake ziyarar aiki a wannan gami. Kafin wannan, ya kai ziyara ga kasashen Cameroon, da Liberiya, da Sudan, da Zambia, da Namibia, da Afrika ta kudu, da kuma Mozambique. (Bilkisu)