
Hu Jintao da Eduardo Joaquim Mulembwe
Shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya bar birnin Maputo, babban birnin kasar Mozambique a ran 9 ga wata, bayan da ya kawo karshen ziyarar aiki a kasar, kuma ya nufi kasar Seychelles, domin ci gaba da ziyararsa a kasashe 8 na Afrika.
A filin jirgin sama, Mr. Armando Emilio Guebuza, shugaban kasar Mozambique ya shirya gagarumin bikin ban kwana ga shugaba Hu Jintao da kuma 'yan rakiyarsa.
A wannan rana kuma, shugaba Hu Jintao ya halarci bikin bude cibiyar gwaji ta fasahohin sha'anin noma da kasar Sin ta ba da taimako ga Mozambique.
A lokacin ziyararsa a Mozambique, shugaba Hu Jintao ya yi shawarwari da shugaba Guebuza, kuma ya gana da Mr. Eduardo Joaquim Mulembwe, shugaban majalisar dokoki na Mozambique. Bayan haka kuma, kasashen Sin da Mozambique sun bayar da hadaddiyar sanarwa. (Bilkisu)
|