|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2007-02-08 21:19:35
|
Shugabannin kasashen Sin da Mozambique sun yi shawarwari
cri
Ran 8 ga wata da dare agogon Beijing, shugaba Hu Jintao na kasar Sin, wanda ya isa birnin Maputo na kasar Mozambique, don yin ziyarar aiki a kasar, ya yi shawarwari tare da takwaransa na kasar Mr. Armando Emilio Guebuza, inda bangarorin biyu suka yi musayar ra'ayoyinsu sosai kan dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, da kuma muhimman batutuwan shiyya-shiyya da na duniya.
Bayan shawarwarin, shugabannin kasashen biyu za su halarci bikin sa hannu kan takardun hadin kai a jere a tsakanin bangarorin biyu, kuma za su gana da manema labaru tare. (Bilkisu)
|
|
|