Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-08 20:31:29    
Ministan harkokin waje na Seychelles yana fatan ziyarar Hu Jintao za ta kai dangantaka tsakanin Sin da kasar zuwa wani sabon mataki

cri
A kwanakin baya, Mr Patrick Georges Pillay, minista mai kula da harkokin waje da hadin kan kasa da kasa na Seychelles ya bayyana cewa, ziyarar da Hu Jintao, shugaban kasar Sin zai yi a kasar Seychelles nan gaba kadan wani babban al'amari ne mai muhimmanci ga tairhin dangantaka a tsakanin kasashen biyu, yana fatan ziyarar za ta kai dangantakar zuwa wani sabon mataki daga duk fannoni.

Yayin da yake karbar ziyarar da manema labaru suka yi masa, ya ce, tun bayan da aka kulla huldar diplomasiya a tsakanin kasashen biyu a shekarar 1976, an yi ta bunkasa huldar nan kamar yadda ya kamata, kuma an sami sakamako a zahiri. Ko da yaushe, kasar Seychelles tana tsayawa kan manufarta game da Sin daya tak a duniya, kuma ta nuna goyon bayanta ga ra'ayoyin bangaren Sin a fagagen kasa da kasa da yawa. Kasar Sin ita ma ta fahimci wahala da matsala da kasar ke fuskanta, kuma ta samar mata da gudummuwa da take bukata. (Halilu)