Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-07 20:45:15    
Hu Jintao ya yi jawabi a Jami'ar Pretoria

cri

A ran 7 ga wata, shugaban kasar Sin Hu Jintao, wanda yake ziyarar aiki a kasar Afirka ta kudu, ya yi wani jawabi mai suna 'Sin da Afirka su kara hadin kai domin kafa wata duniya mai jituwa' a Jami'ar Pretoria ta kasar, inda shugaba Hu ya bayyana ra'ayin kasar Sin a kan kara sada zumunci da ke tsakaninta da Afirka da kafa wata duniya mai jituwa.

Shugaba Hu ya ce, kara sada zumunci a tsakanin Sin da Afirka da kara hadin kai a tsakaninsu da raya sabuwar dangantakar abokantaka a tsakaninsu bisa manyan tsare tsare daga fannoni daban daban ya zama wani buri ne na jama'ar Sin da Afirka da kuma bukatar zamanin yau.

Bayan da ya yi jawabi, shugaba Hu ya amsa tambayoyin da daliban Jami'ar Pretoria suka yi masa, ya ce, kasar Sin tana son kara samar da kyakkyawar dama ga daliban Afirka wajen koyon al'adun kasar Sin.

Da ake tabo magana a kan matsalar Durfur, shugaba Hu ya ce, kasar Sin tana tsayawa tsayin daka cewa, a warware matsalar Darfur ta hanyar yin shawarwari a kan siyasa bisa tushen girmamawa mallakar kai na kasar Sudan tare da yin la'akari da bangarori daban daban.(Danladi)