|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2007-02-06 17:47:34
|
Hu Jintao ya tashi daga kasar Namibiya zuwa kasar Afrika ta kudu
cri
Shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya bar birnin Windhoeak na kasar Namibia a ran 6 ga wata agogon wurin, bayan da ya kawo karshen ziyarar aiki a kasar, kuma ya nufi Afrika ta kudu domin yin ziyarar aiki a kasar.
Shuagaba Hifikepunye Pohamba na kasar Namibia ya shirya gagarumin bikin ban kwana ga shugaba Hu a filin jirgen sama.
Kafin ya bar kasar, shugaba Hu ya gana da Sam Nujoma, shugaban jam'iyyar SWAPO, kuma tsohon shugaban da ya kafa kasar, bayan haka kuma ya halarci taron tattaunawa na wakilan masana'antun kasar Sin da ke kasashen Afrika.
Kasar Namibia ita ce ta 5 a cikin jeren kasash 8 na Afrika da shugaba Hu yake ziyarar aiki a wannan gami. Kafin wannan, ya kai ziyara ga kasashen Cameroon, da Liberiya, da Sudan, da kuma Zambia. Kuma zai kai ziyara a kasashen Mozambique, da Seychelles. (Bilkisu)
|
|
|