|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2007-02-05 18:38:55
|
(Sabunta)Shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya kawo karshen ziyararsa a kasar Zambia
cri
Shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya kawo karshen ziyarar aiki ga kasar Zambia, kuma ya bar birnin Lusaka, babban birnin kasar a ran 5 ga wata da sassafe agogon wurin, ya nufi kasar Namibia, domin ci gaba da ziyararsa ga kasashe 8 na Afrika.
A filin jiragen sama, shugaba Levy Mwanawasa na kasar Zambia ya shirya gagarumin bikin ban kwana ga shugaba Hu Jintao.
A lokacin ziyararsa ga Zambia, shugaba Hu ya yi shawarwari tare da shugaba Mwanawasa na kasar, kuma ya gana da Mr. Amusaa K-Mwanamwambwa, shugaban majalisar dokoki, da tsoho shugaba Kenneth David Kaunda na kasar Zambia.
Bayan haka kuma, bangarorin biyu sun bayar da hadaddiyar sanarwa, inda suka bayyana cewa, za su karfafa hadin kai a tsakanin kasashen biyu a fannoni daban daban.
Kasar Zambia ita ce ta 4 a cikin jeren kasash 8 na Afrika da shugaba Hu yake ziyarar aiki a wannan gami. (Bilkisu)
|
|
|