Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-26 15:06:58    
Kungiyar salon-iyo ta kasar Sin na zura ido kan taron wasannin Olympic na Beijing

cri

Jama'a makaunata, ko kuna sane da cewa, har kullum kungiyar salon-iyo ta kasar Japan tana kan matsayin gaba a Asiya kuma tana cikin jerin kungiyoyi masu karfi a duniya. Amma, a gun taron wasannin motsa jiki na Asiya da aka gudanar da shi kwanakin baya ba da dadewa ba a Doha, hedkwatar kasar Qatar, kungiyar salon-iyo ta kasar Sin ta samu lambobin zinariya guda biyu a fannin irin wannan wasa na tsakanin mata biyu-biyu da kuma na tsakanin kungiya-kungiya, wato ke nan a karo na farko ne kungiyar kasar Sin ta lallasa ta kasar Japan a gagarumar gasa ta kasa da kasa. Kuma a kusan sa'I daya ne shahararriyar mai koyar da salon-iyo mai suna Imura Masayo wadda kuma aka lakaba mata " Sarauniyar salon-iyo" ta kasar Japan ta amsa gayyatar da kungiyar salon-iyo ta kasar Sin ta yi mata don ta zama malamar koyarwa ta kungiyar din. Wannan lamari dai ya shaida cewa lallai kungiyar salon-iyo ta kasar Sin ba ta so a bar ta baya a gun taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008, wato ke nan za ta yi kokarin kafa tarihi a gun taron wasannin.

Madam Yu Li, wata jami'ar kula da wasan salon-iyo na babbar hukumar wasan motsa jiki ta kasar Sin ta jaddada, cewa dalilin da ya sa kungiyar salon-iyo ta kasar Sin ta samu maki mai faranta mutane a gun taron wasannin Asiya na Doha, shi ne domin wannan 'yan wasa na kungiyar nan suka yi namijin kokari cikin shekaru da dama. Sa'annan ta fadi, cewa har kullm mukan kara karfin da muke da shi da kuma kyautata fasahohin da muke da su a fannin wasan salon-iyo.

Daga baya Madam Yu Li ta bayyana, cewa sabbin 'yan wasa sun maye gurbin tsoffin 'yan wasa na kungiyar salon-iyo ta kaksar Sin bayan taron wasannin Olympic na Aden a shekarar 2004. Lallai wadannan sabbin 'yan wasa suna da kyawawan halayen jikuna kuma suna da kyaun-gani; Kazalika, suna kusan kwarewa wajen iyon; Dadin dadawa, 'yan wasan wannan kungiya suna yin horaswa cikin himma da kwazo, wato ke nan sukan yi horaswa na tsawon sa'o'I 8 a kowace rana, kusan babu lokacin hutu gare su cikin duk shekara.

An labarta, cewa wani muhimmin dalilin da ya sa kungiyar salon-iyo ta kasar Sin ta samu manyan nasarori kamar haka, shi ne domin babbar hukumar wasan motsa jiki ta kasar Sin ta kara zuba jari wajen horar da 'yan wasan kungiyar da kuma kashe kudade masu yawan gaske don gayyatar malaman koyarwa na ketare bisa kwangila don su koyar da 'yan wasan a nan kasar Sin. Madam Yu Li ta furta, cewa: ' A da, an tafi an bar mu baya a Asiya da kuma duniya a gannin irin wannan wasa domin rashin isasshen kudin da muka samu tun bayan da aka kafa babbar hukumar wasannin motsa jiki ta kasar. Don haka, mun ga tilas ne mu dogara bisa malaman koyarwa na kanmu wajen horar da 'yan wasan salon-iyo.'

Amma, daga baya gwamnatin kasar Sin ta kara ware kudade ga wasan salon-iyo, sai kungiyar wasan salon-iyo ta kasar ta soma gayyatar kwararrun malaman koyarwa ne kasashen waje bisa kwangila don su horar da 'yan wasa a kasar Sin. Bayan shekarar 2000, kungiyar wasan salon-iyo ta kasar Sin ta soma gayyatar jami'ai a fannin fasaha na hadaddiyar kungiyar wasan iyo ta kasa da kasa bisa kwangila don su zo nan kasar Sin su ba da shawarwari ga 'yan wasan salon-iyo. Ban da wannan kuma, kungiyar kasar Sin ta gayyaci tsohuwar babbar mai koyar da 'yan wasan salon-iyo ta kasar Canada wato Madam Sheilagh Croxon bisa kwangila don ta tsara shirin gwada wasan salon-iyo ga kungiyar kasar Sin. Hakan ya taka muhimmiyar rawa ga kungiyar wasan salon-iyo ta kasar Sin wajen inganta karfin da take da shi.

Madam Yu Li ta kara da cewa, tare kusantowar gagarumin taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008, lallai kungiyar wasan salon-iyo ta kasar Sin na bukatar samun kwararrun malaman koyarwa don taimakonta wajen tabbatar da burinta na cimma matsayi na uku har farko a duniya daga matsayi na biyar a halin yanzu. Bisa wannan dalili ne, aka gayyaci Madam Imura Masayo, shahararriyar mai koyar da wasan salon-iyo daga kasar Japan don ta yi horaswa a na kasar Sin.

Mutane na zura ido kan cewa ko kungiyar wasan salon-iyo ta kasar Sin za ta zama zakara a gun taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008? Kuma shin ko Madam Imura Masayo za ta kafa sabon tarihinta na koyar da wasan salon-iyo?( Sani Wang )