Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-09 15:24:44    
Idan iyaye mata su fi bai wa yara kwarin gwiwa wajen cin abinci, yara za su samu kiba fiye da kima

cri

Bisa wani sakamakon nazari da kasar Amurka ta bayar, an ce, mai yiyuwa ne samun kiba fiye da kima ga yara yana da nasaba da hanyoyin cin abinci da su kan bi bisa bukatar iyayensu mata. Idan iyaye mata suna da kiba fiye da kima, to yaransu sun fi saukin karbar shawarwarinsu wajen cin abinci da yawa.

Bisa labarin da mujallar ilmin likita na yara ta kasar Amurka ta bayar, an ce, manazarta na jami'ar Michigan ta kasar Amurka sun gudanar da wani bincike kan iyaye mata 71 da yaransu 71 wajen ci abinci daban daban iri hudu. Abinci iri biyu daga cikinsu su ne waina da soyayyen dankali da su kan ci a zaman yau da kullum, kuma abincin iri biyu daban su ne mooncake da soyayyun 'ya'yan itatuwa da kayan lambu wadanda ba safai a kan ci ba. Haka kuma a cikin wadannan iyaye mata, sulusi daga cikinsu suna da kiba fiye da kima, yayin da yaran da yawansu ya kai kusan kashi 12.5 cikin dari suna da kiba fiye da kima.

Sakamakon binciken ya bayyana cewa, ko da yake iyaye mata masu kiba ba su bai wa yaransu kwarin gwiwa wajen cin abinci sau da yawa idan an kwatanta shi da yadda iyaye mata ba su da jiki sosai suka yi, amma yaran iyaye mata masu kiba sun fi karbar shawararin iyayensu mata wajen cin abinci idan an kwatanta su da yara na iyaye mata da ba su da jiki sosai. Haka kuma ana iya ganin irin wannan bambanci a bayyane yayin da ake cin abincin ba safai a kan cin irinsa ba, kashi 67 cikin dari daga yaran iyaye mata masu kiba suna son cin irin wannan abinci bayan da iyayensu mata suka ba su kwarin gwiwa, amma wannan jimla ta kai kashi 52 cikin dari kawai ga yara na iyaye mata da ba su da jiki sosai.

Manazarta sun yi hasashen cewa, dalilin da ya sa yaran iyaye mata masu kiba suka fi karbar shawararin iyayensu shi ne wadannan yara sun fi son mayar da martani kan muhalli wajen cin abinci, haka kuma watakila sabo da shawarar da iyaye mata masu kiba suka bayar wajen cin abinci ta sha bamba da wadda iyaye mata da ba su da jiki sosai su kan yi. Bugu da kari kuma manazarta sun gano cewa, iyaye mata masu kiba wadanda yaransu ke da nauyin jiki sosai sun fi son ba wa yara kwarin gwiwa wajen ci abincin da ba su taba ci ba, kuma ba su son bai wa yara kwarin gwiwa wajen cin abincin da su kan ci. Sabo da haka manazarta suna ganin cewa, watakila iyaye mata masu kiba suna ganin cewa, akwai abubuwan gina jiki mafi yawa a cikin abincin da ba safai su kan ci irinsa ba.(Kande)