Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-27 16:12:05    
Likitocin kasar Sin sun yi suna sosai a tsibirin Zanzibar na kasar Tanzania

cri

Tun bayan da kasar Sin ta aika da kungiyar jiyya ta farko ga kasar Algeria a watan Afril na shekara ta 1963, ya zuwa yanzu kasar Sin ta riga ta tura masu jiyya kusan dubu 16 zuwa kasashe da yankuna 47 na Afirka domin taimaka wa fararren hula na Afrika. A 'yan kwanakin nan da suka gabata, wakilinmu ya je kasashen Tanzania da Seychelles da dai sauran kasashen Afirka domin zantawa da kungiyar jiyya ta kasar Sin da ke gudanar da ayyukansu a wuraren. To, a cikin shirinmu na yau, za mu yi muku bayani kan likitocin kasar Sin da suka yi suna sosai a tsibirin Zanzibar da ke kasar Tanzania.

Tsibirin Zanzibar da ke kasar Tanzania ya shahara sosai a duk duniya sakamakon samar da clove, amma tsibirin yana daya daga cikin wurare mafi taulaci a duniya, kuma matsayinsa wajen jiyya yana baya sosai. A shekaru fiye da 40 da suka gabata, akwai wata kungiyar jiyya ta kasar Sin da ke gudanar da ayyukanta a kan tsibirin.

Asibitin Mnazi Nmoja da kungiyar jiyya ta kasar Sin ke ciki wani asibitin gwamnati ne a kan tsibirin Zanzibar, amma yanayinsa daga dukkan fannoni ya yi daidai da asibitin da ke gundumar kasar Sin. Shugaba na karo na 21 na kunigyar Wang Penglai ya bayyana cewa,

"Na'urorin asibiti na wurin suna baya, kuma ana karancin magunguna sosai, ban da wannan kuma babu kwararrun likitoci da masu jiyya a asibitin. Sabo da haka likitocin kasar Sin suna takawa muhimmiyar rawa wajen aiki. Idan suka gamu da mutanen da suka kamu da cututuwa masu tsanani, to za su bukaci taimakonmu, shi ya sa ko wane dan kungiyar yana cikin shirin zuwa asibiti don taimakawa mutane masu fama da ciwo a ko wane lokaci."

Tsibirin Zanzibar wani wuri ne inda aka fi samun cututukan malariya da kwalara da kanjamau. Sabo da wadannan cututuka suna yaduwa cikin matukar sauri, shi ya sa a cikin tiyatar da ta fi zubar da juni da yawa, mutane mafi yawa su kan gamu da cututukan. Madam Sui Cancan, babbar likitar ilmin kula da lafiyar mata da haihuwa ta gaya mana cewa,(???)

"A wata rana, wata nus ta gaya mana cewa, wata mace mai ciki da ta kamu da ciwon kanjamau za ta haihu. Amma sabo da ta gamu da matsala wajen haihuwa, shi ya sa halin da take ciki yana da tsanani sosai. A wancan lokaci, ni ma na ji tsoro sosai, sabo da hannuna ya ji rauni a 'yan kwanakin nan da suka gabata, idan na yi mata tiyata, to mai yiyuwa ne zan kamu da ciwon kanjamau. Amma idan ba a yi mata tiyata nan da nan ba, wannan mace da jaririn da ke cikinta za su mutu. Ganin haka na tsai da kudurin yin mata tiyata cikin gaggawa. Abin farin ciki shi ne tiyatar ta samu nasara sosai."

Ban da rashin samun isassun kayayyaki a kan tsiribin Zanzibar, har ma da kyar ake iya samar da ruwa da wutar lantarki yadda ya kamata. Amma a cikin wannan hali, 'yan kungiyar jiyya ta kasar Sin suna gudanar da ayyukansu har fiye da shekaru 40 ba tare da nuna damuwa ba. Mazauna tsibirin sun nuna girmamawa da godiya gare su sosai sabo da kyakkyawar kwarewarsu wajen aiki. Moliu A. Jape, wani likita na wurin ya bayyana cewa,

"likitocin kasar Sin suna da kirki, kuma sun yi tamkar rashin jin gajiya har abada lokacin da suke aiki. Ko wanensu kwararre ne, ba kawai mu likitocin wurin muke ganin haka ba, har ma likitocin kasashen waje da ke wurin su kan yi musu tambayoyi wajen ilmin likita. Yanzu 'yan kungiyar jiyya ta kasar Sin sun riga sun zama iyalai da abokanmu. Muna fatan za a ci gaba da inganta zumuncin da ke tsakaninmu. "

Jama'a masu sauraro, yanzu sai ku huta kadan, bayan haka kuma za mu karanta muku wani bayani kan cewa, an samu sakamako mai kyau wajen hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka a fannin ilmin koyar da sana'o'i da fasaha.(Kande)