Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-10 17:25:30    
Shugaban kasar Eritrea ya yaba wa taron koli na Beijing

cri
A kwanan nan, shugaban kasar Eritrea Isaias Afwerki ya nuna yabo sosai ga taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka da kuma dangantakar da ke tsakanin kasashen Eritrea da Sin.

A ran 8 ga wata, shugaba Isaias wanda ya halarci taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka ya koma birnin Asmara, babban birnin kasar Eritrea, ya yi zantawa da manema labarai na gidan talebijin na kasar a filin jiragen sama, inda ya bayyana cewa, an kasance da zumuncin gargajiya tsakanin Sin da Afirka. A gun wannan taron koli, kasar Sin ta yi alkawari ga kasashen Afirka masu yawa wajen kara ba da taimako ga Afirka a fannonin siyasa da tattalin arziki da kuma zamantakewar al'umma, ta yadda za ta sa kaimi ga bunkasuwar nahiyar Afirka. Ko shakka babu wannan zai inganta da ci gaba da bunkasa hadin kai da zumuncin gargajiya da ke tsakanin Afirka da Sin.

Ban da wannan kuma shugaba Isaias ya ce, a cikin shekaru 15 da suka gabata, ana raya dangantakar da ke tsakanin kasashen Eritrea da Sin daga dukkan fannoni. Kasar Sin ta samar da taimako sosai ga Eritrea domin nuna goyon baya gare ta wajen samun bunkasuwar tattalin arziki. (Kande Gao)