Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-10 12:06:02    
Masana'antun lardin Zhejiang na kasar Sin suna gudanar da harkokinsu a kasashen duniya

cri

Lardin Zhejiang wani lardi ne mai sukuni da ke a kudu maso gabashin kasar Sin. Tun can zamanin da, 'yan kasuwa na lardin suna da al'adar gudanar da harkokinsu a ko ina cikin kasar Sin. Yanzu kuma ba ma kawai masana'antun lardin nan suna gudanar da harkokinsu a gida ba, har ma suna neman samun damar gudanar da harkokinsu a kasashen duniya.

Birnin Luanda, hedkwatar kasar Angola wani birni ne mai ni'ima da ke a bakin tekun Atlantic. A lokacin zafi na shekarar nan, kamfanin gine-gine mai suna "Huafen" na birnin Ningbo na lardin Zhenjiang da wani kamfnin gina gidaje na kasar Angola sun rabbata hannu a kan yarjejeniya game da gina gidajen kwana da gine-ginen ofisoshi, a wani wuri mai fadin kadada 5.3 na birnin Luanda. Madam Qin Lijun, mataimakiyar babban direktan kamfanin "Huafen" ta bayyana cewa, yawan kudi da za a kashe wajen yin aikin gina gidajen kwana da gine-ginen ofishoshi a wannan wuri na birnin Luanda zai kai dalar Amurka miliyan 120. Ta kara da cewa, "a yanayin zafi da ya wuce, kamfaninmu ya rattaba hannu a kan yarjejeniyar gina gidajen kwana da gine-ginen ofisoshi a kasar Angola. A shekarar bara ne, kamfaninmu ya riga ya fara gudanar da ayyukan gine-gine a kasar Thailand, kuma ya kammala yawancin ayyukan gine-ginen nan. Bisa matsayinsu na kamfanoni masu zaman kansu ko na gwamnati, idan hali ya yi, sai su yi kokarin fadada kasuwanninsu a gida da waje."

Yanzu, manyan kamfanoni na lardin Zhejiang wadanda ke kokarin zuba jari wajen kafa masana'antu a kasashen waje, kullum sai kara karuwa suke yi. Bisa kidayar da hukumar kula da harkokin tattalin arziki da cinikayar waje ta lardin Zhejiang ta yi, an ce, yawan kudin jari da kamfanonin lardin suka zuba a kasashen waje ya kai dalar Amurka miliyan 800 a shekarar bara. Masana'antu da suka zuba jari sun hada da masaka da masakar tufafi da masana'antun sarrafa kayayyaki masu aiki da wutar lantarki da magunguna da kayayyakin sadarwa da sauransu.

Ba ma kawai masana'antun lardin Zhejiang suna gudanar da harkokinsu a kasashen waje domin kara neman kudi da samun kasuwanni masu yawa ba, har ma domin sanya kayayyaki da suke fitarwa, su kara shahara a kasashen waje. Malam Lai Changda, babban manaja na babban kamfanin yin cinikayyar waje mai suna "Yiwan" na lardin Zhejing yana ganin cewa, ko da yake kamfaninsa karami ne, amma yana shirin kafa masana'antun kamfaninsa a kasar Jamus. Ya ce, "za mu iya sanya kayayyakinmu da su kara shahara a kasashen duniya, ta hanyar kafa masana'antunmu a kasar Jamus. Muna son sanya wani irin samfurin kayan aiki na zamani da muke fitarwa za su kara shahara a nahiyar Turai. Ko da yake masana'antun kamfaninmu ya shahara sosai a birninmu mai suna "Ningbo", amma birnin "Ningbo" wani karamin wuri ne, sabo da haka muna shirin kafa masana'antunmu a kasashen waje."

Ban da wadannan kuma, kamfanonin lardin Zhejiang suna zuba jari wajen kafa cibiyoyin binciken fasaha ta inganta kayayyaki a kasshen waje. Madam Luo Weihong, mataimakiyar shugaban hukumiyar kimiyya da fasaha ta lardin Zhejiang ta bayyana cewa, kafa cibiyoyin binciken fasaha ta inganta kayayyaki wata hanya ce mai kyau da ake bi wajen daga matsayin kimiyya da fasaha na masana'antun lardin Zhejiang. Ta kara da cewa, "ana fama da karancin kwararru a lardinmu na Zhejiang. Sabo da haka yayin da ake bunkasa harkokin tattalin arzikinmu ta hanyar kimiyya da fasaha, wajibi ne, mu hada kanmu tare da kasashen waje. A cikin irin wannan hali ne, ya kamata, gwamnatinmu ya kara nuna goyon baya ga inganta hadin kai a tsakanin lardinmu da kasashen waje a fannin fasaha da kirkirowa da kafa cibiyoyin binciken fasaha ta inganta kayayyaki."

Masu aikin masana'antu na lardin Zhejiang suna ganin cewa, babbar manufarsu game da zuba jari a kasashen waje ita ce neman samun nasara domin su da kasashe da suke zuba jari. (Halilu)