Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-09 11:43:52    
Wata jaridar Kenya ta ci gaba da bayar da labari kan sakamakon da aka samu a taron koli na Beijing

cri
Ran 8 ga wata, jaridar The Standard ta kasar Kenya ta ci gaba da bayar da labari kan sakamakon da aka samu a taron kili na Beijing na dandalin tattaunawa kan harkokin hadin kai a tsakanin Sin da Afrika.

Jaridar ta ce, Mr. Mwai Kibaki, shugaban kasar Kenya, ya gama ziyararsa a kasar Sin ba da dadewa ba, kuma ya koma birnin Nairobi na kasar Kenya ya bayar da wata sanarwa cewa, taron koli na Beijing wata muhimmiyar alama ce da ke tabbatar da hadin kai a tsakanin Sin da Afrika nan gaba. A cikin sanarwar ya ce, gwamnatin kasar Sin ta riga ta yi alkawari cewa, za ta nuna goyon baya ga shirye-shirye na kasar Kenya da kuma na sauran kasashen Afrika, za ta kara karfin zuba jari ga Afrika. A waje daya kuma, Mr. Kibaki ya bayyana cewa, gwamnatin Kenya za ta cika alkawarin da ta yi a cikin lokacin taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan harkokin hadin kai a tsakanin Sin da Afrika, wanda zai amfanawa bangarorin Sin da Afrika. (Bilkisu)