Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-08 16:41:39    
Wasu kafofin watsa labaru na kasashen Afirka sun yaba wa taron koli na Beijing

cri

Bayan da aka rufe taron koli na dandalin tattaunawa a kan hadin kai a tsakanin Sin da Afirka, bi da bi ne kafofin watsa labaru na Zimbabuwei da Burkina Faso da kuma Aljeriya da dai sauran kasashen Afirka suka bayar da sharhohinsu, inda suka yaba wa taron koli na Beijing sosai, sun ce, wannan taro yana da muhimmiyar mana'a a tarihi, kasashen Afirka suna fatan za su yi amfani da wannan kyakkyawar dama domin samun bunkasuwa ta hanyar hadin kai da kasar Sin a kan tattalin arziki da cinikayya.

Babbar jarida ta farko ta kasar Zimbabuwei wato jaridar Herald ta bayar da wani sharhi a ran 6 ga wata cewa, 'a halin yanzu, kasar Zimbabuwei tana kara jawo hankalin kasar Sin sosai. Ya kamata kasarmu ta yi amfani da wannan dama wato bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin domin samun bunkasuwarmu.'

Wata jaridar Burkina Faso ta buga wani labari mai lakabi haka, 'lokacin bazara sa samun bunkasuwa cikin hadin gwiwa', ta ce, kasar Sin ta bayyana cewa, za ta samu bunkasuwa tare da kasashen Afirka, idan babu zaman lafiya da bunkasuwar Sin da Afirka, to, ba za a iya samun zaman lafiya da bunkasuwa a duk duniya ba.

Jaridar gwamnati ta kasar Aljeriya wato 'El Moudjahid' ta bayyana cewa, taron koli na Beijing ba kawai ya zama wani muhimmin abu a tarihin dangantakar Sin da Afirka ba, har ma ya zama wani babban abu da ke jawo hankulan duniya.(Danladi)