Shugaban kasar Afirka ta kudu, Thabo Mbeki, wanda ya zo kasar Sin don halartar taron koli na dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka da kuma yin ziyara a kasar Sin, ya bayyana cewa, ma iya cewa, sabuwar huldar abokantaka da ke tsakanin Sin da Afirka ta ba da 'sabon ma'auni' wajen kullawa da kuma bunkasa hulda da kasashe masu tasowa, wanda ya kamata kasashen yammacin duniya su yi koyi da shi.
A ran 7 ga wata, jaridar 'The Star' ta Afirka ta kudu ta buga wani rahoton da wakilinta ya aika mata daga birnin Beijing dangane da hirar da aka yi da shugaban kasar, inda Mr.Mbeki ya ce, hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Afirka ya kafu ne bisa tushen moriyar juna, kuma idan hadin gwiwar zai iya taimakawa wajen farfado da Afirka, to, lalle ne ya kamata kasashe masu ci gaba na yammacin duniya su yi la'akari da yin koyi da tsarin hadin gwiwar.(Lubabatu)
|