Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-08 09:01:42    
Hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Afirka ba 'sabon mulkin mallaka' ba ne, in ji shugaban Zambia

cri
A gun wani taron manema labaru da aka shirya ran 7 ga wata a nan birnin Beijing, shugaban kasar Zambia, Levy Patrick Mwanawasa, wanda ya zo nan kasar Sin domin halartar taron koli na dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka, ya musanta furuci na wai 'hadin gwiwar da kasar Sin ke yi a Afirka tamkar wani sabon mulkin mallaka ne ta kafa a Afirka', kuma a cewarsa, hadin gwiwar ya sami gindinsa ne bisa tushen zumuncin gargajiya da kuma moriyar juna.

Game da rahotannin da wasu kafofin yada labarai suka bayar na cewa, wai taimaka wa Zambia wajen bunkasa albarkatun kasa da kasar Sin ke yi aiki ne na kwace kuma mulkin mallaka ne na karo na biyu, Mr.Mwanawasa ya ce, bunkasa albarkatun kasa ba kwace ba ne, balle ma a ce 'mulkin mallaka'. Ya ce, kasar Sin ta ba da dimbin taimako ga Zambia wajen yaki da talauci da samar da guraben aiki da kyautata zaman rayuwar jama'ar kasar dai sauransu, jama'ar Zambia ba za su manta da taimakon da kasar Sin ta ba ta ba tare da son kai ba.(Lubabatu)