Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-07 21:38:37    
Taron koli na Beijing zai ba da tasiri mai yakini kan bunkasuwar Afirka, a cewar shugaban Senegal

cri
Ran 6 ga wata, a birnin Dakar, hedkwatar kasar Senegal, shugaban kasar Senegal Abdoulaye Wade ya yi wa kafofin yada labaru bayanin cewa, tabbas ne sakamakon da aka samu a gun taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da Afirka za su ba da tasiri mai yakini kan bunkasuwar kasashen Afirka.

Mr. Wade, wanda ya koma gida bayan da ya halarci taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, ya bayyana cewa, taron koli na Beijing ya ci nasara sosai, kasar Sin ta tsai da kudurin ninka yawan taimakon da za ta ba kasashen Afirka har sau daya bayan shekaru 3, ta kuma yafe basussuka ga dukan kasashen Afirka masu fama da talauci da suka ci basussuka da yawa da kuma kasashe mafiya fama da talauci, wadanda suka kulla huldar diplomasiyya a tsakaninsu da kasar Sin, irin wadanda basussuka basussuka ne da gwamnatin kasar Sin take binsu ba tare da neman kudin ruwa ko kadan ba, kuma bisa yarjejeniyoyin da aka daddale a da, wajibi ne a mayar da su kafin karshen shekarar 2005. Kasar Sin za ta kuma taimaki Kungiyar Tarayyar Afirka wajen gina babbar cibiyar taro, za ta ba da sukolashif din na gwamnati ga daliban Afirka masu dalibta 4000 a ko wace shekara a cikin shekaru 3 masu zuwa, a maimakon dalibai 2000 na yanzu. Dukan wadannan matakan da kasar Sin za ta dauka sakamako ne da aka samu a gun taron koli na Beijing, kuma za su amfana wa ci gaban Afirka a nan gaba.(Tasallah)