Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-07 21:01:09    
Shugaban kasar Kenya ya nuna yabo sosai ga sakamakon da aka samu a gun taron koli na Beijing tsakanin Sin da Afirka

cri
A ran 7 ga wata, shugaban kasar Kenya Mwai Kibaki wanda ya halarci taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka ya yi bayani bayan da ya koma birnin Nairobi, babban birnin kasar Kenya, cewa taron koli na Beijing ya zama tamkar ishara ce wajen tabbatar da dangantakar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka a nan gaba, kuma ya samar da sabbin zarafofi ga bunkasuwar Afirka.

A ranar, bayan da Shugaba Kibaki ya isa birnin Nairobi, ya yi jawabi a filin jiragen sama, cewa a gun taron koli, kasar Sin ta yi alkawarin bayar da taimako ga kasar Kenya kan gina muhimman ayyukan yau da kullum da karfafa kwarewar kasa da kiwon lafiya da kuma ayyukan jin dadin jama'a. Haka kuma ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Kenya za ta cika alkawarin da ta yi a cikin sanarwar taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka domin amfana wa jama'ar Sin da Afirka. A waje daya kuma yana fatan jama'ar Kenya za su iya yin amfani da zarafofi iri daban daban wajen samun bunkasuwa sakamakon sabuwar dangantakar abokantaka tsakanin Sin da Afirka bisa manyan tsare-tsare.(Kande Gao)