Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-07 20:26:04    
Matar shugaban kasar Niger ta ziyarci kamfanin da ke harhada maganin Cotecxin a kasar Sin

cri

A ran 7 ga wata da safe, matar shugaban kasar Niger Fati Tandja ta ziyarci kamfanin harhada magunguna mai suna Cote da ke yin maganin Cotecxin domin magancen zazzabin cizon sauro na kasar Sin.

Bisa gabatarwa da mutane da ke raka ta suka yi, an ce, Madam Tandja tana da matukar sha'awar aikin jin dadin jama'a, musamman ma ta fi mai da hankali a kan ci gaban aikin shawo kan zazzabin cizon sauro, sabo da haka aka nada mata wani suna wato 'matar shugaba mai yaki da zazzabin cizon sauro'. Maganin Cotecxin da kamfanin harhada magunguna mai suna Cote da ke yi ya shahara sosai a Afirka, sabo da haka, Madam Tandja ta bukaci yin ziyara a wannan kamfani musamman.

Da Madam Tandja ta san cewa, wannan kamfani yana shirin kafa wata masana'anta a kasar Tanzania, kuma zai samar da maganin a Afirka, to, ta yi fata cewa, kamfanin zai yi la'akari a kan kafa masana'antu a Afirka da ke magana da Faransanci, musamman a kasar Niger. Ta ce, 'ta haka, za a iya kusantar da maganin da mutane ke bukata.'(Danladi )