Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-07 18:21:53    
Hu Jintao ya yi shawarwari da ganawa tare da wasu shugabannin kasashen Afirka

cri

A ran 7 ga wata, daya bayan daya shugaban kasar Sin Hu Jintao ya gana da takwaransa na kasar Masar Muhammed Hosni Mubarak da na kasar Burundi Pierre Nkurunziza, da na kasar Somaliya Abdullahi Yusuf da kuma na kasar Zambia Levy Patrick Mwanawasa.

Dukkan wadannan shugabanni sun halarci taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka da aka rufe a birnin Beijing ba da jimawa ba. Yayin da yake yin shawarari tare da shugaba Mubarak, shugaba Hu ya bayyana cewa, taron koli na Beijing ya zama tamkar sabuwar ishra ce ta hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka don moriyar juna. Bangaren Sin zai yi shawarwari tare da bangaren Masar domin aiwatar da sakamako mai kyau da aka samu a gun taron, da kuma gudanar da ayyukan share fare sosai ga taron ministoci na karo na hudu da za a yi a kasar Masar, ta yadda za a ci gaba da samun bunkasuwar da ke tsakanin Sin da Afirka.

A nasa bangare, shugaba Mubarak ya bayyana cewa, taron koli na Beijing ya samu nasara daga dukkan fannoni. Bangaren Masar zai hada kansa tare da banganren Sin domin sa kaimi ga samun dauwamammiyar ci gaban dangantaka tsakanin Sin da Afirka lami lafiya.

Yayin da yake ganawa da shugabannin kasashen Burundi da Somaliya da kuma Zambia, shugaba Hu ya bayyana cewa, wannan taron koli ya zama tamkar wata muhimmiyar ishara ce ta dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka, kuma bangaren Sin ya gabatar da sabbin matakai a jere ne wajen hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka domin nuna goyon baya ga kasashen Afirka wajen karfafa kwarewarsu ta raya kansu. Wannan ya shaida sahihin buri na Sin da Afirka wajen zama abokan arziki har abada.

Shugabannin uku sun bayyana cewa, kasashe daban daban na Afirka za su yi kokari tare da Sin wajen ingiza bunkasuwar sabuwar dangantakar abokantaka tsakanin Sin da Afirka bisa manyan tsare-tsare. (Kande Gao)