Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-07 17:19:08    
Hu Jintao ya gana da shugabannin kasashen Burundi da Somaliya da kuma Zambia bi da bi

cri

A ran 7 ga wata, a birnin Beijing, daya bayan daya ne hugaban kasar Sin Hu Jintao ya gana da takwaransa na kasar Burundi Pierre Nkurunziza, da na kasar Somaliya Abdullahi Yusuf da kuma na kasar Zambia Levy Patrick Mwanawasa.

Wadannan shugabanni uku sun halarci taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka da aka rufe a ran 5 ga wata a birnin Beijing. A cikin ganawar, shugaba Hu ya bayyana cewa, wannan taron koli ya zama tamkar wata muhimmiyar ishara ce ta dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka, kuma bangaren Sin ya gabatar da sabbin matakai a jere ne wajen hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka domin nuna goyon baya ga kasashen Afirka wajen karfafa kwarewarsu ta raya kansu. Wannan ya shaida sahihin buri na Sin da Afirka wajen zama abokan arziki har abada.

Shugabannin uku sun bayyana cewa, an dasa kyakkyawar aya ga taron koli na Beijing, kuma wannan ya shaida cewa, zumuncin da ke tsakanin jama'ar Sin da Afirka da dangantakar da ke tsakaninsu sun samu nasara. Kasashe daban daban na Afirka za su yi kokari tare da Sin wajen ingiza bunkasuwar sabuwar dangantakar abokantaka tsakanin Sin da Afirka bisa manyan tsare-tsare. Ban da wannan kuma shugabannin uku sun bayyana cewa, za su tsaya tsayin daka kan kasar Sin daya tak a duniya.(Kande Gao)