A ran 6 ga watan nan a nan birnin Beijing , Wu Bangguo , Shugaban Majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya gana da shugabannin kasashe 4 na Afrika , wato shugaba Mubarak na kasar Masar da shugaba Boutiflika na kasar Algeria da shugaba Mbeki na kasar Afrika ta kudu da firayin minista Ramgoolam na kasar Mauritius .
Mr. Wu da shugabannin kasashen 4 sun nuna yabo sosai ga taron kolin Beijing kan dandalin hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da Afrika wanda aka rufe shi ba da dadewa ba . Gaba daya suna ganin cewa , taron koli na wannan karo ya sami nasara , kuma yana da muhimmanci sosai kuma yana da babbar ma'ana ga tarihin hadin gwiwar zumunci tsakanin Sin da Afrika . Sun kuma bayyana cewa , za su tabbatar da yarjejeniyoyin da aka cim mawa a gun taron kolin , kuma za su ciyar da yalwatuwar dangantakar tsarin musamman da sabbin abokai tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika . (Ado)
|