Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-06 21:19:09    
Taron koli na Beijing zai ciyar da hadin guiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Afirka gaba daga duk fannoni

cri
A ran 6 ga wata, ministan kasuwanci na kasar Sin Bo Xilai ya bayyana a birnin Beijing cewa, matakai 8 da shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya bayar a gun taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin guiwar Sin da Afirka za su amfana wa yunkurin ciyar da hadin guiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka gaba da kyau cikin sauri.

Mr. Bo ya ce, wadannan matakai 8 hakikanan manufofi ne. Ba tantama, za su sa kaimi sosai wajen ciyar da hadin guiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Afirka gaba. A cikin 'yan shekarun da suka wuce, yawan kudaden cinikayya da aka samu tsakanin Sin da kasashen Afirka ya samu karuwa cikin sauri. Yanzu, dandalin yin hadin guiwar tattalin arziki da cinikayya tsakaninsu ya fi samun kyautatuwa da girma, bangarorin biyu za su iya kara samun sabbin hadin guiwa da bunkasuwa bisa sabon tushe.

Mr. Bo ya kuma jaddada cewa, bangaren kasar Sin zai aiwatar da manufofin kara yin hadin guiwa tsakaninsa da bangaren Afirka yadda ya kamata. Kuma zai taimaki kasashen Afirka kan yadda za su iya neman bunkasuwa da kansu. A waje daya kuma, bangaren kasar Sin yana son hada kan kasashen Afirka domin kara yin hadin guiwa a sabbin fannonin tattalin arziki da cimma burin neman samun bunkasuwa irin ta moriyar juna tare. (Sanusi Chen)