Bayan da kasashen Algeriya da Sudan da Afirka ta Tsakiya da Saliyo sun daddale takardun bayani tare da kasar Sin bi da bi a ran 5 ga wata wajen amincewa da cikakken matsayin takarar harkokin kasuwanni na kasar Sin, a ran 6 ga wata, kasar Masar ta sanar da amincewa da cikakken matsayin takarar harkokin kasuwanni na kasar Sin.
A ranar, a birnin Beijing, ministan kasuwanci na kasar Sin Bo Xilai da Rasheed Mohammad Rasheed, ministan masana'antu da yin cinikayya da kasashen waje na kasar Masar sun rabbata hannu a kan takardar bayani kan cewa, kasar Masar ta amince da cikakken matsayin takarar harkokin kasuwanni na kasar Sin, da kuma inganta hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu kan tattalin arziki da cinikayya.
Bisa takardar, kasar Masar ta amince da cikakken matsayin takarar harkokin kasuwanni na kasar Sin. Bangarorin biyu sun tsai da kudurin karfafa hadin gwiwa tsakaninsu a fannonin cinikayya da zuba jari da neman kwangilar ayyuka da kuma horar da ma'aikata, ta yadda za a iya ci gaba da inganta dangantakar da ke tsakanin Sin da Masar kan tattalin arziki da cinikayya.
Ta haka ya zuwa yanzu, kasashen Afirka 14 sun riga sun amince da cikakken matsayin takarar harkokin kasuwanni na kasar Sin.(Kande Gao)
|