Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-06 16:38:36    
Kasashe 4 na Afrika sun amince da matsayin kasar Sin na cikakken tsarin tattalin arziki na kasuwanni

cri
Ran 5 ga wata, Mr. Wei Jianguo, mataimakin ministan kasuwanci na kasar Sin ya cimma takardun fahimtar juna da Mr. Rachid Harraoubia, ministan harkokin ba da ilmin jami'a, da nazarin kimiyya na kasar Algeria, kuma shugaban bangaren Algeria na kwamitin kula da harkokin tattalin arziki da ciniki na Sin da Algeria, da Mr. Al-Zubair Ahmed, ministan sha'anin kudi, da na tattalin arzikin kasar Sudan, da Mr. Come Zoumara, ministan harkokin waje na kasar Afrika ta tsakiya, da Mr. Momodu Koroma, ministan harkokin waje da hadin kan duniya na kasar Saliyo daya bayan daya.

Ministocin kasashen 4 suna ganin cewa, tun bayan da kasar Sin ta aiwatar da manufar gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, sai kasashen duniya suka amince da sakamakon da ta samu wajen gine-ginen tsarin tattalin arziki na kasuwanni. Sabo da haka, gwamnatocin kasashen hudu sun amince da matsayin kasar Sin na cikakken tsarin tattalin arziki na kasuwanni.

Mr. Wei Jianguo ya yi yabo ga gwamnatocin kasashen 4 da su amince da matsayin kasar Sin na cikakken tsarin tattalin arziki na kasuwanni. Ya jaddada cewa, a gun taron kolin na dandalin tattaunawa kan harkokin hadin kai a tsakanin Sin da Afrika, Mr. Hu Jintao, shugaban kasar Sin ya sanar da matakan da kasar Sin ta dauka wajen karfafa hadin kai da kasashen Afrika, bangaren Sin zai tabbatar da su, kuma zai ba da taimako ga kasashen Afrika wajen kara karfin bunkasuwa da kansu. (Bilkisu)