Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-05 22:34:12    
Za a kara raya sabuwar dangantakar abokantaka irin ta manyan tsare-tsare a tsakanin Sin da kasashen Afirka

cri

A ran 5 ga wata da yamma, a gun bikin rufe taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin guiwar kasar Sin da kasashen Afirka, an bayar da "Sanarwar taron koli ta Beijing ta dandalin tattaunawa kan hadin guiwar kasar Sin da kasashen Afirka". Shugaba Hu Jintao na kasar Sin da firayin minista Zinawi Meles na kasar Habasha da shguaba Hosni Mubarak suka karanta wannan sanarwa tare. Wannan sanarwa tana bayyana kafuwar sabuwar dangantakar abokantaka irin ta manyan tsare-tsare tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka.

Shekarar da muke ciki shekara ce ta cikon shekaru 50 da kafuwar dangantakar diplomasiyya a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. A wananan shekarar da take da ma'ana ta musamman, tun daga farkon wannan shekara, gwamnatin kasar Sin ta bayar da "Takardar bayyana manufofin da kasar Sin ke dauka kan kasashen Afirka", inda ta bayyana cewa, tana fatan kafa sabuwar dangantakar abokantaka a tsakaninta da kasashen Afirka. Mr. Hosni Mubarak, shugaban kasar Masar ya karanta cewa, "A hukunce ne muke sanar da cewa, kasashen Sin da Afirka mun tsai da kudurin kafuwar sabuwar dangantakar abokantaka irin ta zaman daidai wa daida da amincewa da juna kan harkokin siyasa da yin hadin guiwa da neman nasara a fannin tattalin arziki tare da kuma fahimtar al'adu juna a tsakaninsu."

A cikin wannan sanarwa, an jaddada muhimmancin kafuwar irin wannan sabuwar dangantakar abokantaka a tsakanin Sin da Afirka. Mr. Mubarak ya ce, "Muna ganin cewa, kafuwar sabuwar dangantakar abokantaka a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka buri daya ne na bangarorin biyu, kuma yana dacewa da moriyarsu duk. Zai kuma amfana wa yunkurin yin hadin guiwa a tsakanin kasashe masu tasowa da tabbatar da zaman lafiya mai dorewa da jituwa a duk duniya baki daya."

A cikin rabin karnin da ya wuce, bangarorin Sin da Afirka sun fi mai da hankali kan yin hadin guiwa a fannonin neman bunkasuwar tattalin arzikinsu da kyautata zaman rayuwar jama'a. To, a cikin sabon halin da ake ciki yanzu, yaya kasashen Sin da Afirka za su kara yin hadin guiwa irin ta moriyar juna, ya zama batun da ya fi jawo hankulan shugabannin kasashen Afirka daban-daban da suka halarci taron koli na Beijing. A gun bikin kaddamar da taron, a madadin gwamnatin kasar Sin ne shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya bayar da sabbin matakan da suke shafar fannoni 8 kan yadda za a kara yin hadin guiwa a tsakanin Sin da Afirka a cikin sabon halin da ake ciki. Mr. Zinawi Meles, firayin ministan kasar Habasha, wato kasa ce da ke shugabantar wannan dandalin tattaunawa kan hadin guiwar kasar Sin da kasashen Afirka tare da kasar Sin, ya karanta wadannan matakai 8, ya kuma ce, "Muna ganin cewa, ana da kyakkyawar al'adar yin hadin guiwa da gama kai a tsakanin Sin da kasashen Afirka. Alakar da ke tsakanin Sin da Afirka tana kasancewa ne a cikin zuciyar jama'arsu. A cikin sabon halin da ake ciki yanzu, kasar Sin da kasashen Afirka suna da buri daya wajen neman bunkasuwa da kuma kusan moriya daya. Makomar yin hadin guiwa a tsakaninsu tana da haske kwarai. Karfafa zumuncin gargajiyada kara yin hadin guiwar moriyar juna a tsakaninsu, hanya ce da ya wajaba da kasashen Sin da Afirka za su bi domin cimma burinsu na neman bunkasuwa."

Kasar Sin da kasashen Afirka dukkansu kasashe ne masu tasowa. Matsayin da kasar Sin ke dauka wajen nuna wa kasashen Afirka goyon baya wajen neman bunkasuwa da kansu yana cikin wannan sanarwa. Mr. Hu Jintao, shugaban kasar Sin ya karanta cewa, "Kasar Sin tana mai da hankali sosai kan yadda kasashen Afirka za su iya gama kansu wajen neman bunkasuwa da daidaita batutuwan Afirka da kansu. A waje daya kuma, kasar Sin tana goyon baya ga kungiyoyin Afirka da kungiyoyin shiyya-shiyya na Afirka da su yi kokari wajen raya tattalin arzikinsu bai daya. Tana kuma nuna goyon baya ga 'Sabon shirin abokantaka na raya Afirka' da kasashen Afirka suke aiwatarwa."

Bayan rufewar taron koli, Mr. Tang Jiaxuan, wakilin majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya gaya wa wakilinmu cewa, wannan taron koli na Beijing zai ciyar da dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka gaba daga duk fannoni. (Sanusi Chen)