Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-05 21:33:32    
An samu sakamako mai kyau a gun taron koli na Beijing tsakanin Sin da Afirka

cri
A ran 5 ga wata, ministan harkokin waje na kasar Sin Li Zhaoxing ya bayyana a birnin Beijing, cewa an samu sakamako mai kyau a gun taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka da aka rufe shi ba da jimawa ba, kuma nasarar da taron koli na Beijing ya samu ta kafa tushe ga sabuwar dagantakar hadin kai tsakanin Sin da Afirka bisa manyan tsare-tsare da take ta samun bunkasuwa.

Haka kuma a gun taron manema labarai da Li Zhaoxing da takwarorinsa na kasashen Habasha da Masar suka kira tare, ya bayyana cewa, an tsara da kuma zartas da "sanarwar taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka" da "shirin aikatawa na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka daga shekara ta 2007 zuwa shekara ta 2009" a gun taron koli na Beijing, inda aka samu ra'ayi daya kan kulla sabuwar dagantakar abokantaka ta hadin kai tsakanin Sin da Afirka bisa manyan tsare-tsare bisa tushen samun daida wa daida da amincewa da juna a fannin siyasa, da hada kai a fannin tattalin arziki don moriyar juna, da kuma yin mu'amala da koyi da juna a fannin al'adu.(Kande Gao)