Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-05 20:43:57    
Kasashen Sin da Afirka za su kara yin hadin guiwa da mu'ammalar tattalin arziki da cinikayya

cri

A ran 4 ga wata da yamma, an yi taron tattaunawa a tsakanin shugabannin Sin da Afrika da wakilan shugabannin masana'antu da kuma taron shugabannin masana'antu na kasar Sin da na kasashen Afirka a karo na biyu. Wannan taro muhimmin sashe ne na taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin guiwar kasar Sin da kasashen Afirka. A gun taron, Wen Jiabao, firayin ministan kasar Sin ya bayar da wani jawabi, inda ya ce, lokacin da ake murnar cikon shekaru 50 da kafuwar dangantakar diplomasiyya tsakanin Sin da kasashen Afirka, gwamnatin kasar Sin ta sanar da jerin sabbin matakai domin kara yin hakikanin hadin guiwa da kasashen Afirka. Tun da haka, kasar Sin da kasashen Afirka za su kara yin mu'ammala da hadin guiwar tattalin arziki da cinikayya a tsakaninsu.

A gun bikin kaddamar da taron, Wen Jiabao ya ce, makomar hadin guiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka tana da haske mai kyau. "Kasar Sin kasa mai tasowa ce mafi girma a duniya, nahiyar Afirka nahiya ce da ke da kasashe masu tasowa da yawa. Za su iya taimakawa juna a fannin tattalin arziki. Za a iya kara yin hadin guiwa domin irin wannan hadin guiwa tana da kyakkyawar makoma. Tabbas ne za mu tsaya kan matsayin zaman daidai wa daida da kara yin hadin guiwa irin ta moriyar juna. Sabili da haka, sakamakon da za mu samu domin yin hadin guiwa a tsakaninmu zai iya moriyar dukkan jama'ar kasar Sin da na kasashen Afirka."

Mr. Wen Jiabao ya ce, kasar Sin da kasashen Afirka suna yin hadin guiwa a tsakaninsu. Kasar Sin tana samar wa kasashen Afirka taimako bisa bukatun da kasashen Afirka suke nema. Bangarorin Sin da Afirka suna tabbatar da kowane aikin taimako tare. Wadannan taimako sun bayar da gudummawa sosai wajen neman bunkasuwar kasashen Afirka. Mr. Wen ya kuma yi kira ga kasashen duniya da su yi kokari tare domin ci gaba da nuna wa kasashen Afirka goyon baya.

Mr. Wen ya ce, "Mu kan yi tsammani cewa, ya kamata a nuna wa juna goyon baya da taimako a tsakanin kasa da kasa. Ba za mu manta da goyon bayan da yawancin kasashen Afirka suka nuna wa kasar Sin wajen tabbatar da cikakken ikon mulki da cikakken yankuna na kasar Sin har abada ba. Muna fatan za mu iya kara yin hadin guiwa irin ta moriyar juna da neman samun nasara tare da kasashen Afirka a sahihanci. Hadin guiwar da ake yi a tsakanin Sin da kasashen Afirka tana cikin budadden hali, muna maraba da sauran kasashen duniya da na kungiyoyin kasa da kasa za su iya kara yin hadin guiwa da kasashen Afirka, kuma za su iya kara samar wa kasashen Afirka goyon baya da taimako."

Jawabin da Mr. Wen ya yi ya samu amincewa daga shugabannin kasashen Afirka da 'yan kasuwa na kasar Sin da na kasashen Afirka wadanda suka halarci taron. A cikin nasa jawabi, shugaba Paul Kagame na kasar Rwanda ya bayyana cewa, kasar Rwanda da kungiyar hada kan kasashen gabashin Afirka har da duk nahiyar Afirka suna fatan za a iya kara yin hadin guiwa a tsakaninsu da kasar Sin a fannonin tattalin arziki da cinikayya. Mr. Kagame ya ce, "Muna koyon fasahohin da kasar Sin ta samu wajen neman bunkasuwa, kuma muna samu moriya da yawa daga alakar dangantaka tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. Za a yi hadin guiwar zuba jari da yin cinikayya a tsakanin kasar Rwanda da kasar Sin. Muna yaba wa gwamnatin kasar Sin domin ba ta buga harajin kwastam ba kan kayayyakin da ake shigar da su daga kasashen Afirka. Muna fatan wanann matakin da ake dauka domin kara bude kasuwannin kasar Sin zai kara bayar da gudummawarsa domin zai shafi yawancin kayayyakin da ake shigar da su daga kasashen Afirka."

Mr. Vincent Ssenyonjo-Bazira, wani dan kasuwa ne na kasar Uganda wanda ke cinikin furannin danye. Mr. Bazira ya ce, yana jin alfahari sosai domin halartar wannan taro. Yana kuma fatan zai iya yin amfani da wannan dama domin sayar da furannin kasar Uganda a kasar Sin. "Dalilin da ya sa na zo wannan taro shi ne neman damar yin kasuwanci. Ina fatan zan iya samun abokan kasuwanci a kasar Sin. Yanzu ana yin hadin guiwar kasuwanci sosai a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. Ina cinikin amfanin gona, musamman ina cinikin furannin danye. Ina son sayar da furannin danye na kasar Uganda a kasuwar kasar Sin.", a cewar Bazira. (Sanusi Chen)