Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-05 18:17:48    
Kasashen Sin da Afirka sun rattaba hannu a kan kwangiloli da jimlar kudadensu ta kai dala biliyan 1.9

cri

A gun bikin rufe babban taro na karo na biyu na 'yan masana'antu na kasashen Sin da Afirka da kuma bikin daddale kwangiloli da aka yi a ran 5 ga wata da safe, gwamnatoci da kamfanoni na kasashen Afirka da kamfanonin kasar Sin 11 sun rattaba hannu a kan kwangilolin cinikayya 14 da jimlar kudadensu ya kai kusan dala biliyan 1.9.

Kasashen Habasha da Masar da Afirka ta Kudu da Nijeriya da Kenya da Ghana da sauransu wadanda yawasu ya kai 11 sun sa hannu a kan wadannnan kwangiloli da suka shafi fannonin gina muhimman ayyukan yau da kullum da fitar da kayayyakin sadarwa da fasahohi da raya albarkatun kasa da inshorar kudi.

Kuma a gun bikin, kungiyar ingiza yin cinikayya tsakanin kasa da kasa ta kasar Sin da kawancen kungiyoyin kasuwanci na Afirka sun daddale yarjejeniyar hadin kai wajen kafa hadaddiyar kungiyar kasuwanci tsakanin Sin da Afirka, da kuma sanar da kafuwar kungiyar.(Kande Gao)