Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-05 18:08:38    
An ba da sanarwar taron koli na Beijing na dandalin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka

cri

Ran 5 ga wata, a nan Beijing, an rufe taron koli na Beijing na dandalin hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. An zartas da 'sanarwar taron koli na Beijing na dandalin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka', a hukunce ne aka sanar da kafa da raya sabuwar dangantakar abokantaka ta muhimman tsare-tsare a tsakanin Sin da Afirka.

Shugaban kasar Sin da ke shugabantar dandalin tattaunawar Hu Jintao da firayin ministan kasar Habasha da ke gama kanta da kasar Sin wajen shirya dandalin tattaunawar Meles Zenawi da kuma shugaban kasar Masar da za ta kira taron ministoci mai zuwa Muhammed Hosni Mubarak su ne suka karanta wannan sanarwa.

Sanarwar ta bayyana cewa, an tanadi yin zaman daidai wa daida da amincewa da juna a fannin siyasa, da hada kai don cin nasara tare a fannin tattalin arziki, da yin mu'amala da koyi da juna a fannin al'adu a cikin sabuwar dangantakar abokantaka ta muhimman tsare-tsare a tsakanin Sin da Afirka. Saboda haka, bangarorin 2 sun tsara matakai daga fannoni 7, ban da karfafa amincewa da juna a fannin siyasa da kara yin mu'amala tsakanin ma'aikata kuma, za su kara yin hadin gwiwa don moriyar juna a tsakaninsu. Za su daidaita sabbin batutuwa da kalubale da za su fuskanta wajen yin hadin gwiwa, bisa dangantakar abokantaka da ke tsakaninsu da kuma moriyarsu ta dogon lokaci.(Tasallah)