Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-05 16:29:21    
An yi taron fuska da fuska na taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka

cri

Ran 5 ga wata, a nan Beijing, an yi taron fuska da fuska na taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, inda aka dora muhimmanci kan yin tattaunawar sanarwar taron koli da shirin ayyuka na shekaru 3 masu zuwa.

Shugaba Hu Jintao na kasar Sin da ke shugabantar dandalin tattaunawar da firayin ministan kasar Habasha da ke gama kanta da kasar Sin wajen shirya dandalin tattaunawar Meles Zenawi sun bakunci wannan taron fuska da fuska daya bayan daya.

Don raya dangantakar abokantaka ta muhimman tsare-tsare ta sabon salo da ke tsakanin Sin da Afirka, shugaba Hu ya sanar da sabbin matakai 8 da kasar Sin za ta aiwatar da su wajen kara hadin gwiwa da Afirka a gun bikin bude taron koli da aka yi a ran 4 ga wata, wadanda suka hada da kara ba da taimako da yafe basussuka da kara karfin horar da ma'aikata da kafa asusun raya Sin da Afirka da dai sauransu. An labarta cewa, muhimmin abin da za a tanada a cikin sanarwar taron koli nan da kuma shirin ayyuka na shekaru 3 masu zuwa shi ne yadda za a aiwatar da wadannan matakai.(Tasallah)