Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-05 12:38:57    
Shugaban kasar Sin ya gabatar da manufofi dangane da bunkasa sabuwar huldar abokantaka a tsakanin Sin da Afirka

cri
A gun bikin bude taron koli na dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka da aka yi a ran 4 ga wata, shugaban kasar Sin ya bayar da jawabi, inda ya gabatar da manufofi da matakai daga fannoni takwas dangane da bunkasa sabuwar huldar abokantaka a tsakanin Sin da kasashen Afirka.

Manufofin dai sun hada da, na farko, za a kara ba da taimako ga kasashen Afirka, ta yadda zuwa shekara ta 2009, taimakon da kasar Sin za ta bayar ga kasashen Afirka zai ninka sau daya bisa na shekarar 2006. Na biyu kuwa, nan da shekaru uku masu zuwa, kasar Sin za ta ba da rancen kudi mai gatanci da yawansa ya kai dallar Amurka biliyan uku ga kasashen Afirka, da kuma ba su rancen kudi mai gatanci na kudin Amurka dalla biliyan 2 wajen shigar da kayayyaki daga kasar Sin. Na uku, don sa kaimi ga kamfanonin kasar Sin da su zuba jari a Afirka, kasar Sin za ta kafa asusun raya Sin da Afirka, wanda yawan kudinsa zai kai dallar Amurka biliyan 5 sannu a hankali, da dai sauransu.

Mr.Meles Zenawi, firaministan kasar Habasha, wato kasar da ke shugabantar dandalin tare da kasar Sin, da kuma shugaban kasar Kongo Brazzaville, Mr.Denis Sassou-Nguesso, su ma sun yi jawabi a gun bikin bude taron. Shugabanni ko kusoshin gwamnatocin kasashen Afirka fiye da 40 sun halarci bikin.(Lubabatu)