A ran 4 ga wata, Kofi Annan, babban sakataren MDD ya bayar da sanarwa, inda ya taya murnar taron koli na dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka wanda aka yi a nan birnin Beijing.
Sanarwar ta ce, har kullum, Sin da Afirka suna magana da murya daya a wajen tabbatar da burinsu daya na bunkasuwa. Wannan taron koli wata muhimmiyar dama ce wajen tabbatar da buri daya na Sin da Afirka da kara ingiza hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa. Kasar Sin ta cimma manyan nasarori a wajen yaki da talauci da kuma tabbatar da dawamammiyar bunkakasuwar tattalin arziki, kuma fasahohin kasar Sin za su amfana wa jama'ar Afirka a wajen fuskantar kalubalen da ke gabansu.(Lubabatu)
|