Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-05 11:06:16    
Kafofin yada labarai na kasashen ketare sun darajanta taron koli na Beijing

cri
A jiya ranar 4 ga wata, an cimma nasarar kira taron koli na dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka, kuma a kwanakin baya a jere, wasu kafofin yada labarai na kasashen ketare sun bayar da bayanai bi da bi, inda suka darajanta taron koli na dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka da kuma taron ministocinsa na karo na uku.

A ran 2 ga wata, jaridar 'daily mirror' ta kasar Zimbabuwe ta bayar da bayanin cewa, ba shakka nahiyar Afirka za ta ci gajiyar taron koli na dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka. A gun wannan taron koli, bangarorin Afirka da Sin za su tattauna yadda za su samar da sharuda masu kyau ga masana'antunsu, ta yadda zai kara taka rawa mai kyau. Tabbas ne amincewa da juna a tsakanin Afirka da Sin da kuma kokarin da suke yi tare zai hau da wata gadar zumunci a tsakanin bangarorin biyu.

Ban da wannan, jaridar Public Opinion ta kasar Sudan, ta bayar da sharhin cewa, taron zai zama wani dandali a tsakanin Sin da kasashen Afirka inda za su iya yin mu'amala da inganta fahimtar juna da kuma ingiza hadin gwiwa a tsakaninsu a fannonin siyasa da tattalin arziki, kuma zai taka muhimmiyar rawa wajen inganta sabuwar huldar abokantaka a tsakanin Sin da Afirka.

Ban da wannan, a ran 3 ga wata, jaridar Togo-presse ta gwamnatin kasar Togo ta bayar da bayanin cewa, kasar Sin ta kulla huldar ciniki mai kyau a tsakaninta da kasashen Afirka. A cikin shekaru sama da gomai da suka wuce, kasar Sin ta kara ba da taimako ga kasashen Afirka, kuma ta inganta hadin gwiwar moriyar juna da kasashen Afirka a fannin tattalin arziki, tana tsayawa a kan kulla sabuwar huldar abokantaka a tsakaninta da Afirka bisa sahihanci da sada zumunta da zaman lafiya da kuma moriyar juna.(Lubabatu)