Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-04 20:13:03    
An bude taron koli na Beijing na dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka

cri

A yau ranar 4 ga wata, an bude kasaitaccen taron koli na dandalin hadin kan Sin da Afirka a nan birnin Beijing, kuma shugabannin Sin da kasashen Afirka 48 da kusoshin gwamnatocinsu ko wakilansu sun halarci wannan taro. Taron dai ya kasance taro mafi kasaita a tsakanin Sin da kasashen Afirka tun bayan da suka kulla huldar diplomasiyya a tsakaninsu a shekaru 50 da suka wuce. A gun taron, shugabannin Sin da Afirka za su bi manufar sada zumunta da zaman lafiya da hadin gwiwa da kuma ci gaba, su tattauna kan yadda za su bunkasa huldar da ke tsakaninsu da kuma kara ingiza hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa. A gun bikin bude taron, shugaban kasar Sin, Mr.Hu Jintao ya yi jawabi, inda ya gabatar da manufofi da matakai daga fannoni takwas dangane da bunkasa sabuwar huldar abokantaka a tsakanin Sin da kasashen Afirka.

A watan Oktoba na shekara ta 2000, gaba daya ne kasar Sin da kasashen Afirka suka ba da shawarar kafa dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka. A cikin shekaru shida da suka wuce, dandalin ya riga ya zama wani tsari mai amfani da kuma wani dandali mai muhimmanci wajen yin shawarwari tsakanin kasashen Sin da Afirka baki daya da kuma yin hakikanin hadin gwiwa a tsakaninsu. Bana shekara ce ta cika shekaru 50 da kulla huldar diplomasiyya a tsakanin Sin da kasashen Afirka. Da yake waiwayen zumuncin da ke tsakanin Sin da Afirka a cikin shekarun nan 50 da suka wuce, shugaban kasar Sin, Mr.Hu Jintao ya ce,'yau zumuncin da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka ya riga ya zauna da gindinsa a zukatan jama'ar bangarorin biyu, kuma dalilin da ya sa zumuncin ya iya cin jarrabawar tarihi da kuma sauye-sauyen yanayin duniya shi ne, sabo da muna tsayawa a kan bin ka'idojin sada zumunta cikin sahihanci da zaman daidaici da goyon bayan juna da kuma samun ci gaba tare a yayin da muke bunkasa huldar da ke tsakaninmu.'

Mr.Hu ya bayyana cewa, don kara bunkasa sabuwar huldar abokantaka a tsakanin Sin da kasashen Afirka, kasar Sin tana son kara inganta huldar siyasa ta amincewa da juna a tsakaninta da kasashen Afirka, su fadada hadin gwiwar tattalin arziki irin ta moriyar juna da samun nasara tare, kuma su habaka mu'amalar al'adu don koyi da juna, su ingiza bunkasuwar duniya cikin daidaici kuma yadda ya kamata, kuma su karfafa hadin gwiwar kasa da kasa don goyon bayan juna.

A madadin gwamnatin kasar Sin ne, Mr.Hu Jintao ya kuma gabatar da manufofi da matakai daga fannoni takwas dangane da kara inganta sabuwar huldar abokantaka a tsakanin Sin da kasashen Afirka. Ya ce,'na farko, za mu kara ba da taimako ga kasashen Afirka, ta yadda zuwa shekara ta 2009, taimakon da kasar Sin za ta bayar ga kasashen Afirka zai ninka sau daya bisa na shekarar 2006. Na biyu kuwa, nan da shekaru uku masu zuwa, za mu ba da rancen kudi mai gatanci da yawansa ya kai dallar Amurka biliyan uku ga kasashen Afirka, da kuma ba su rancen kudi mai gatanci na kudin Amurka dalla biliyan 2 wajen shigar da kayayyaki daga kasar Sin. Na uku, don sa kaimi ga kamfanonin kasar Sin da su zuba jari a Afirka, za mu kafa asusun raya Sin da Afirka, wanda yawan kudinsa zai kai dallar Amurka biliyan 5 sannu a hankali.'

Meles Zenawi, firaministan kasar Habasha, wato kasar da ke shugabantar dandalin tare da kasar Sin, ya yi jawabi a gun bikin bude taron cewa, taron koli na Beijing da aka shirya ya shaida wa duniya niyyar Sin da Afirka wajen kulla sabuwar huldar abokantaka a tsakaninsu. Ya ce,'ya kamata a mai da hankali a kan bunkasuwar tattalin arzikin Afirka a yayin da ake bunkasa sabuwar huldar abokantaka a tsakanin Sin da Afirka. Bunkasuwar Sin cikin lumana da saurin karuwar tattalin arzikinta da kuma kyautatuwar matsayinta a duniya duk sun shaida cewa, ya kamata a mai da hadin gwiwar tattalin arziki a matsayin wani muhimmin abin da ke cikin sabuwar huldar abokantaka a tsakanin Sin da Afirka.'

Ban da wannan, a gun bikin bude taron, shugaban kasar Congo Brazzaville, wato kasar da ke shugabantar kungiyar tarayyar Afirka a halin yanzu, Mr.Denis Sassou-Ngues, shi ma ya yi jawabi, inda ya yi nuni da cewa, manufofi da matakai da shugaba Hu Jintao ya sanar daga fannoni takwas sun bayyana ra'ayin kasar Sin na kara bunkasa hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Afirka, don haka, ya nuna godiya a madadin shugabannin kasashen Afirka da ke halartar taron. Ya kara da cewa,'Ina imani da cewa, taron kolin nan zai kara bunkasa da kuma inganta huldar abokantaka da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka. Muna kuma imani da cewa, muna iya cimma burin nan.(Lubabatu)