Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-04 18:28:51    
Taron koli na dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka zai bunkasa hadin gwiwar Afirka da Sin

cri
A yayin da yake hira da wakilinmu a ranar 3 ga wata a nan birnin Beijing, ministan harkokin masana'antu da kasuwanci na kasar Nijer, Habi Mahamadou Salissou ya bayyana cewa, taron koli na Beijing na dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka zai kara ciyar da huldar aminci da hadin gwiwa da ke tsakanin bangarorin biyu gaba.

Mr.Salissou wanda ke halartar taron dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka a nan birnin Beijing, ya ce, shugabanni ko kusoshin gwamnati na kasashen Afirka sama da 40 sun hadu a nan birnin Beijing, don halartar taron koli na Beijing na dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka, sun gane ma idonsu kan bunkasuwar kasar Sin, kuma suna neman hadin gwiwa a tsakanin bangarorin biyu, abin nan zai kara ciyar da huldar aminci da hadin gwiwa a tsakanin Afirka da Sin gaba kwarai da gaske.

Mr.Salissou ya kuma yi fatan ta taron nan, za a kara samun kamfanonin kasar Sin da su je Nijer don zuba jari da kuma kafa masana'antu, gwamnatin Nijer ma za ta yi kokarin samar da sharuda ga hadin gwiwar da ke tsakanin bangarorin biyu.(Lubabatu)